`Yan Fim Din Jahar Katsina Zasu Gana Da Gwamna Masari

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0

‘YAN FIM ƊIN JIHAR KATSINA ZA SU GANA DA GWAMNA MASARI.

Daga Isah Bawa Doro

A yau da misalin ƙarfe 11:00pm na dare wasu daga cikin ‘yan fim na jihar Katsina za su gana da mai girma gwamnan Katsina RT. Hon. Aminu Bello Masari a gidan gwamnatin jihar Katsina.

An zaɓi mutum goma 15 a matsayin wakilan da za su wakilci duk wani mai ruwa da tsaki a cikin harkar fim ɗin Hausa da ke Katsina.

Sai dai tun kafin aje ko’ina an fara samun tsegumi tare da guna-guni game da tafiyar, ya yin da wasu ke ganin cewa za a je a ari bakin su a ci masu albasa ba tare da an sanar da su abin da za a faɗa ba tun da an ce ‘yan fim za a wakilta.

A gefe guda kuma wasu na ganin ‘yan ina da fim ne aka ɗauka domin yin wakilcin. Akwai ma wanda ya ce rufa-rufa ce kawai tafiyar ta su.

Da alamu dai ziyarar ta su za ta bar bayar da ƙura ganin irin yadda aka fara samun ƙorafe-ƙorafe daga wasu jiga-jigan masu harkar.

*Shin me zai biyo bayan ziyarar ta su?

*Su waye wakilan da za su wakilcin?

*Wace waina za a toya?

*Me zai biyo bayan ziyarar?

Ku biyomu a Mujallar fim ta wannan watan domin jin cikakken labarin.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.