Yadda Ta Kaya A Wajan Tattara Sakamakon Zaben Gwale

0 111

YADDA TA KAYA A WURIN TATTARA SAKAMAKON ZABEN GWALE.

DA NA GABA AKAN GA ZURFIN RUWA: SIYASAR DABA A GWAMNATIN JIHARMU?

Ina wannan rubutun cike da fatan zai amfanar da duk wani dan siyasa da ma wanda ba dan siyasa ba.

A ‘yan kwanakin nan korafe-korafe sun yi yawa akan zargin da ake wa gwamnatin HE Dr. Abdullahi Umar Ganduje na amfani da dabanchi wajan tallata manufar su a siyasan ce.

A jiya asabar 10/02/2018 na ga abubuwan ban mamaki da ban tsoro a wajan tattara sakamakon zaben kananan hukomomi na karamar hukumar Gwale da aka sa za’ayi a “Islamic Centre” ta Gwale.

ABUBUWAN DA SUKA BANI MAMAKI:

A bayan an gama zabe a mazabu, hukumar KANSIEC ta gaza ta tattara sakamakon mazabu a kowace mazaba kamar yadda aka saba. Saboda haka wasu mazabun sai aka taho da su Islamic Centre. Mun yi musu kyakkyawan zaton cewa watakila yanayi na wutar lantarki ko tsaro ne yasa suka yanke a tattara sakamakon a waje daya amma daga baya sai abubuwa suka fara fitowa na ban mamaki.

Da farko wani jigo a Gandujiyya ya shigo wajan yana sanarwa kowa ya fita daga wajan taron amma bamu tan ka ba.

Daga bisa ni sai jami’an tsaro su ma suka nemi kowa ya fita. Bayan tattaunawar mu da su sun gamsu duk ” returning officer” na mazaba ko na karamar hukuma za su tsaya a wajan.

Bayan wani lokaci sai wani daga cikin jigon APC ya sake zuwa da maganar kowa ya fita. Bayan tattaunawa tsakanin mu da su mun amince tsakanin mu da su da a sa mar da waje a cikin Islamic Centre a tattara sakamakon mazabu kafin ayi na karamar hukuma.

Ana cikin haka sai wani jami’in tsaro da ake kira “DPO”, ban sani ko na Gwale ne ba, yace kowa ya fita. Shi ma bayan tattaunawa dashi ya fahimce ni. Daga bisani sai ya nemi mu zauna da kantoman Gwale, Mal. Sunusi Kani, wani jigon gandujiyya da wasu wadanda ban iya tuna su ba.

Bayan nayi musu bayani, DPO da kantoma duk sun ce sun fahimce ni amma shi wannan jigon sai yace su ba ka’ida suke so ba. So suke su sanar da zabe kawai “inda suka ci 2,000 su mai da ita 10,000”.

 

Mun masa bayanin cewa zamu jira shi KANSIEC returning officer na LG ya fada mana da bakin sa cewa shi sakamakon zai fada kawai ba tare da anyi collation na mazaba dana LG ba.

Idan har yayi haka zamu nuna rashin yardar mu a fili idan bai gyara ba zamu kyale shi ya yi abinda yake so. Mu kuma zamu dau matakin da ya dace.

Bayan an gama wannan kai komon sai wani dan jam’iyyar APC ya kira ni ya bani shawara da mu fita daga wajan saboda jagoran gandujiyya na karamar hukuma zai zo wajan kuma baya san yaga wani dan PDP a wajan. Yana tsoratar mana a bin da zai faru idan yazo ya tarar bamu bar wajan ba.

Na ji dadin shawarar amma ban dauka ba saboda taci karo da wakilcin da muke yi a wajan.

Duk da haka, domin kaucewa faruwar fitina, na nemi na karbi result sheets na mazabu, su kuma su fita daga wajan.

Amma a dai dai wannan lokacin sai muka ji hayaniya har da harba tear gas saboda haka sai nai magana da wannan DPO din akan cewa ina so wakilan mazabu su fita amma a lokacin bai dace su fita ba, saboda haka muna neman ya basu kariya. Ya amince kuma ya basu kariyar.

Komawa ta dakin taron ke da wuya sai wasu gungun ‘yan jagaliya suka shigo tare da wannan jagoran. Suna shigowa sai suka hau mu da duka, ni da Mal. Sunusi Kani. Abinda ya fi bani mamaki shine dukan har da shi wannan jagoran. Ni ya doke ni da hannunsa.

ABUBUWAN DA SUKA BANI TSORO:

Tashin hankalin da siyasa zata jawo idan ya zama jagaliyanci da dabanci ba iya ‘yan kwaya ne kawai ba har da wadanda ake wa kallon su manya ne masu fada a ji. Shi wannan jagoran na gandujiyyar duk da yana da shugabanci tudu uku amma wannan bai hana shi ya mai da kansa dan jagaliya ba mai siyasar dabanci ba.

Shugabane na mulki, shugaba ne a siyasance, sannan basarake ne wanda ko ba kujerar mulki jagora ne a al’umma.

Idan mutane masu wannan siffar ba sa jin kunyar yin siyasar jagaliya da dabanci akwai ban tsoro na irin yadda siyasar kano zata zama anan gaba.

Akwai ban tsoro yayin da duk wanda ya ke ji ya isa zai dau matakin jagaliya da dabanci, ko yana gwamnati ko ba ya gwamnati, domin kare muradun sa na siyasa ko dan cin mutuncin abokin hamayya.

Na biyu, da yawan ‘yan siyasa suna cewa sun shiga siyasa ne domin su gyara ta amma daga karshe sai kaga tarbiyyar su tana kara lalacewa.

A cikin wajan da wannan ta’annati ya faru akwai ‘yan jam’iyyar APC da nake ganin mutuncin su kuma nake girmama su.

Musamman wadanda karatun addini ya fara hada mu da su kafin siyasa.

Amma a bin ban tsoro siyasa ta juyar da tarbiyyar su tai munin da ba sa iya kallon wannan mutuntakar da alakar, duk da akwai hanyoyi da da ma, da duk wani mai hankali da tarbiyya, zai hana faruwar hakan kuma ya cimma burin sa.

Akwai ban tsoro idan zamu samu kan mu a yanayin da masu ilmin addini zasu goyi bayan irin wannan jagaliyar da dabanci. A yau she ne gyaran zaizo?

Abu na uku, shine duk wannan jagaliyar da dabancin an yi shine a gaban jami’an tsaro da ma’aikatan KANSIEC.

Duk da ya zama wajibi mu yabawa jami’an tsaro saboda bawa wasu daga cikin wakilan PDP na mazabu kariya da kuma dakile kokarin hana shigowar wasu ‘yan daba wajan taron domin su kori ‘yan PDP.

Fatan mu shine jami’an tsaro da KANSIEC za suyi amfani da da damar da doka ta basu na dau kan mataki akan abinda ya faru.

Zai zama a bin ban tsoro idan jami’an tsaro da ma’aikatan KANSIEC za su goyi bayan irin wannan jagaliyancin da dabancin saboda ma su yi suna da goyan bayan gwamnati.

Akwai ban tsoro idan wadanda za a kaiwa kuka domin kawo daukin gyara za su zama haka.

Shin ba ma tsoron halin da al’umma za ta shiga idan ba wanda zai tsaya ya tabbatar doka tayi aikinta?

Daga karshe wannan kalubale ne ga duk wani dan siyasa da ma wanda ba dan siyasa ba. Idan muka bari irin wannan salon siyasar na jagaliyanci da dabanci ya dore, ba wanda ba zai dana sani ba tun daga kan jami’an tsaro, shugabannin gwamnati, ‘yan siyasa, malamai da sauran al’ummar Kano.

Daga na gaba akan gane zurfin ruwa!!!

Kuma kowa ya gyara ya sani!!!

Mansur Ahmad Zubair Esq.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com