Yadda Aka Yiwa Wata Matan Aure Tsirara Bisa Laifin Zina A Enugu

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0

Yadda Aka Yiwa Wata Matan Aure Tsirara Bisa Laifin Zina A Enugu
__¥__
*
Rahotanni daga karamar hukumar Aninri da ke jihar Enugu sun nuna cewa al’ummar yankin sun dauki tsauraran mataki a kan wata Matan aure da aka kama tana zina d tsohon saurayinta inda aka yi mata tsirara ita da saurayinta.

Wani wanda al’amarin ya auku a kan idonsa, Mista Calistus Ogbo ya ce, lamarin ya auku ne a yankin Amokwe bayan da saurayin matar ya je gidanta bayan mijinta ya fita, amma kuma wata makwabciyarsu ta sanar da mijin abin da ke faruwa.

Mista Calistus ya kara da cewa, mijin ya samu nasarar kama Kwarton tare da matarsa, lamarin da ya harzuka mutanen yankin bisa abin da suka kira Babban laifi inda suka yanke shawarar yi mata tsirara sannan shi Kwarton aka rataya masa hoton miji da matan, ana yawo da shi cikin garin.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.