| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Tofa Wata Sabuwa Zuwa Ga Adam A Zango

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


1 1,237

Zuwa Ga ADAM ZANGO

Marubuci Hafiz Mohd Shuwaki.

08144613030

08022999691

Ban taba jin ina sonka ba sai da na fara ganinka a wajan Bikin haihuwar  Manzon Allah ( S.A.W ) amma yanzu nafi sanka akan Duk wanda baya son mauludi wannan yasa naga ya kamata in yaba maka kuma in karfafeka akan hakan.

Maulidi abune mai kyau ka cigaba da yi, kuma ina baka shawara kayiwa annabi ( S.A.W ) waka ko kuma ince  ka koma mawakin Annabi domin Allah yayi maka baiwar waka, ka kula da wadannan shawarwarin da nake baka zasu karamaka daukaka Duniya Da Lahira.

Kana zuwa wajan taruka da yawa amma baka taba ganin inda aka nunama soyayya ba kamar wajen maulidi.

Ya kamata wataran ka Hada maulidi a gidanka don nuna farin cikin haihuwar Annabi ( S.A.W ).

Idan kayi maulidi zakaga jama’ar da baka taba gani ba domin wallahi sai kayi mamakin yawan mutanen da zaka gani, kayi gaggawar yin wannan aikin alherin kafin wani dan wasan hausan ya rigaka, Ni da  nake baka wannan shawara sai naje wajen maulidinka tare da almajirai na.

Zango kayi hakuri da sukar da makiya maulidin Annabi suke maka domin kaje wajan maulidi, Ai ya isheka sheda cewa su makiyan Annabi ne domin kasha zuwa wajen Rawa ko Waka ko Sinima ko Studio ko wajan wani biki, amma ban taba jinsu sunce maka bakayi dai-dai ba, Sai da aka fara yin maka cari, kada maganarsu ta baka tsoro, Ka Manta da su makiyan Annabi ne kuma naji dadin bidiyon da akayi da kayi musu akan ba wanda ya isa ya rabaka da Annabi.

Idan sakona yazo gareka ka kira wannan Lambar

08022999691

Domin baka wasu shawarwarin wadanda bazasu rubutu A nan ba.

Allah ya kara maka daukaka. Allah ya Fifitaka a cikin masana’antar fim din hausa.

Dan Allah Ku tura wannan sakon zuwa ga ADAM A ZANGO.

SHIN MAI ZAKUCE
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

1 Comment
  1. Anonymous says

    Gaskia hafiz abunda kaiyi kayi dadai allah ya saka maka

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com