Sanata Saraki Ya Karbi Bakuncin Kannywood (Hotuna)

0

SARKI YA GA SARAKI

Sanata Saraki Ya Karbi Bakoncin Su Ali Nuhu

Shugaban majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki ya karbi bakoncin wasu daga cikin ‘yan fim din Hausa a jiya.

Wasu daga cikin ‘yan fim din wadanda Sanatan ya gana da su sun hada da Ali Nuhu, Tijjani Faraga, Salisu Aliyu (Chali) da Maryam Halilu.

Bayan nuna farin cikin sa da ziyarar, shugaban majalisa na Dattijai ya yi alfahari da masana’antar ta Kannywood, inda ya bayyana yadda matasan maza da mata ke kokarin bunkasa harshen Hausa sannan kuma suna da milyoyin jama’ar da suke kallon finafinansu.

” Yaba muku ya zama dole sannan kuma ayi muku jinjina kan yadda kuka mai da hankali wajen bunkasa wannan sana’a da ganin karbuwar sa ga miliyoyin mutane sannan samar da aikin yi da masana’antar ta yi wa matasa da dama”, cewar Sanatan.

Haka kuma ya bayyana farin cikin sa kan yadda matasa maza da mata suke dogaro da kansu ta hanyar harkar finafinan Hausa.

#Rariya
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.