| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Sam Allardyce Zai Koma Eberton

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0 60

Kungiyar kwallon kafa ta Eberton ta sake karkatawa wajen duba yuwuwar daukar tsohon mai koyar da kungiyoyin Bolton da Newcastle da ingila wato Sam Allardyce a matsayin kociyanta sakamakon halin kaka-ni-ka-yi da ta shiga a wannan kakar.

Kungiyar ta ta sake bijirowa da bukatar samo sabon kociya ne cikin gaggawa bayan kashin da ta sha a gidan Southampton ranar Lahadi da ci 4-1 a gasar firimiya wasan sati na 13

Allardyce ne mutum na farko da aka yi tsammani zai gaji Ronald Koeman, wanda aka kora ranar 23 ga watan Oktoba, amma ya fito fili ya ce ya janye bayan da Eberton ta yi jinkirin nemansa.

Eberton wadda zawarcin da ta yi na neman kociyan Watford Marco Silba ya ci tura, ta yi rashin nasara a wasa biyar cikin bakwai tun lokacin da ta kori Koeman daga aiki.

Allardayce mai shekara 63 ba ya rike da kpwacce kungiya ko yin wata harka a wata kungiyar wasan kwallon kafa tun lokacin da ya bar Crystal Palace a karshen kakar da ta wuce.

Allardyce ya ceto Crystal Palace daga faduwa daga gasar firimiya, bayan da ya bar aikin horar da tawagar Ingila a watan Satumba na shekarar 2016 bayan wasa daya kawai.

Eberton ta sallami Koeman dan kasar Holland daga aiki bayan da kungiyar ta koma ta 18 a gasar firimiya, sakamakon cin da Arsenal ta bi ta har gida ta yi mata 5-2.

Kociyan kungiyar na matasa ‘yan kasa da shekara 23 Dabid Unsworth, wanda ya taka leda a kungiyar a matsayin dan wasan baya, shi ne ke jagorantartar kungiyar a matsayin na riko tun bayan korar Koeman.

Unsworth Ya yi nasarar dago Eberton din zuwa matsayi na 16, bayan da ta samu maki hudu a wasa hudu na firimiya

Bukatar babban mai hannun jari a kungiyar Farhad Moshiri da shugabanta Bill Kenwright ta daukar sabon kociya ta kara kamari ne bayan casa su da Atalanta ta yi a gidanta 5-1 a gasar kofin Turai ta Europa ranar Alhamis, kuma bayan wannan suka je gidan Southampton ta lallasa su daci 4-1 a ranar Lahadi
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com