|| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Rikicin APC A Kano: Kwankwaso Ya Zargi Buhari

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0 373
  • Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani 

Sanata Kwankwaso yayi wadannan kalaman ne biyo bayan wata zungureriyar wasikar da sakataren jam’iyyar APC na kasa ya aike zuwa jihar wadda a ciki ya tabbatar da Injiniya Basie Yahaya Karats a matsayin shugaban jam’iyyar APC na riko a jihar Kano.

Injiniya Karats, wanda ake damfara shi da dan gaban goshin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, wanda kuma ya karbi ragamar tafiyar da jam’iyyar APC daga Yerima Abdullahi Abbas; biyo bayan murabus da yayi yan kwanaki kadan da nada masa rigar kwamishina a jihar.

Kwankwaso ya kara da cewar “muna da masaniyar wata kuskuniyar sirrin karkashin kasa daga shugaban kasa Buhari ta hanyar mai taimaka masa a sha’anin hulda da kafafen yada labarai na gidajen rediyo, Ibrahim Shaaba Sharada, da wasu na kusa dashi, wajen cire shugaban APC da muka zaba a jihar, Haruna Umar Doguwa, ba tare da wata hujja daga kundin tsarin jam’iyyar APC ba.

“bisa ga wannan, baki daya mun yi watsi da wannan matakin kuma muna bayyana cewa ba zamu taba amincewa da shi ba. Haka zalika, muna bayyana wa yan kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar APC na kasa kan cewa ba su tattauna komai dangance da yanayin wannan al’amari ba, saboda haka an yanka ta tashi”. Inji shi.

Sai dai a wani martani da fadar Shugaban kasa ta fitar a jiya, ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bashi da wata alaka da cire Umar Doguwa a matsayin Shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano.

Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun mai Magana da yawun shugaban Kasa Buhari, Malam Garba Shehu.

Malam Garba Shehu ya ce, wannan martani sun fid dashi ne sakamakon wasu kalamai da wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar Kano suka yi, wadanda

kuma ake kyautata tsammanin suna tare ne da Kwankwaso. “Fadar Shugaban Kasa na sanar da cewa duk wasu zargi da ake yi na kokarin sa Shugaba Buhari a rigimar jam’iyyar APC ta Kano, ba gaskiya bane” in ji Garba Shehu.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com