| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Real Madrid Na Zawarcin Hazard Da Azpilicueta

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0 235

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Rahotanni daga birnin Madrid suna cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana zawarcin yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard dan kasar Belgium da Azpilicueta na kasar sipaniya domin su koma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Kungiyar Real Madrid dai sun dade suna zawarcin dan wasa Hazard kusan shekaru uku baya sakamakon irin kokarin dad an wasan yakeyi a kungiyarsa da kuma kasarsa ta Belgium.

A kakar wasan data gabata dai Hazard ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar firimiya ta kasar ingila sannan kuma a wannan shekarar ma yazura kwallaye 9 kawo yanzu a wasannin daya bugawa kungiyar kuma kungiyar tasa tana buga gasar zakarun turai.

Ceser Azpilicueta, dan wasan baya ne wanda kungiyar ta Chelsea ta siyo shi daga kungiyar Marseille ta kasar faransa a shekara ta 2012 sai dai yanzu dan wasan yana daya daga cikin yan wasan da suke taimakawa kungiyar sakamakon kungiyar yanzu tana amfani dashi a wurare daban daban kuma yana kokari.

Azpilicueta, yabuga wasanni 252 a kungiyar sakamakon kokarin da yakewa kungiyar sai dai kungiyar Real Madrid tana ganin idan tasamu dan wasan zai taimakawa kungiyar a bangaren dama a yan wasan baya saboda dan wasan kungiyar Dani Carbahal yana yawan zuwa rauni kuma Azpilicueta yana iya buga wasa a tsakiyar baya.

Sai abune mai wahala kungiyar ta Chelsea ta siyar day an wasan a watan Janairun shekarar nan mai kamawa sai dai watakila Real Madrid ta hakura sai zuwa karshen kakar da ake ciki.

Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai Zidane ya taba bayyana cewa Hazard babban dan wasa ne kuma zaiso ace suna aiki a kungiya daya.




Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com