|| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Nijeriya Za Ta Sha Kashi A Hannun Argentina — Menotti

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0 134

Tsohon mai koyar da ‘yan wasan kasar Argentina da ya jagoranci kasar wajen lashe kofin duniya a shekarar 1978 Luis Menotti ya ce, kai tsaye tawagar kasar za ta samu maki uku a rukunin da ta fada a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a badi.

Argentina na cikin rukuni guda da Nijeriya, kuma a ranar 26 ga watan Junin 2018 ne kasashen biyu za su fafata a Rasha a gasar wadda ala fitar da jadawalin yadda za a buga kowanne wasa.

Tarihi ya nuna cewa, sau hudu Argentina da Nijeriya suka hadu a matakin rukuni a gasar cin kofin duniya, kuma Argentiana ce ke samun nasara a kan Nijeriya da bambacin kwallo guda.

Tsohon kocin ya ce, ba zai yi mamaki ba idan Croatia ta casa Argentina amma a cewarsa, babu shakka kasar za ta samu maki akan Iceland da Nijeriya a mataki rukuninsu na D.

A cikin watan jiya ne, Najeriya ta doke Argentina da ci 4-2 a wasan sada zumunta amma masharhanta na cewa, wannan ba wani abu ba ne idan aka kwatanta da fafatawar da za su yi a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Shi ma mai koyar da yan wasan na kasar Argentina, Jorge Sampaoli ya bayyana cewa dole sai ya sake shiri wajen ganin ya samu nasara a kan Nijeriya.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com