| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Nigeria: APC da PDP na cacar baki kan wahalar mai

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0 143
Tun bayan shan kaye a zaben shekarar 2015, jam’iyyar PDP ke sukar mulkin APC

Jam’iyyar APC mai mulki a Nigeria ta zargi Jam’iyyar adawa ta PDP da amfani da karanci man fetur da ake fuskanta don ba ta mata suna a idon ‘yan kasar.

A wata sanarwa da kakakin Jami’iyyar Mallam Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, APC ta ce tana sa ne da wahalhalun da ‘yan Nigeria suka shiga sakamakon karancin man fetur musamman a lokacin bukukuwan kirsimeti.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati tana iyakacin kokarinta don kawo karshen matsalar nan bada jima wa ba.

Sai dai APC ta ce abun takaici ne yadda PDP take amfani da karancin man wajen bata sunan gwamnatin APC da jami’anta, abun da jam’iyyar ta ce ba siyace mai kyau ba.

Tun da farko jam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da ya samar wa ‘yan kasar man fetur ya daina zargin dillalan man da haddasa karancin da ake fuskanta.

A wata sanarwa daga kakakinta Kola Ologbondiyan, PDP ta ce tun da shugaba Buhari ya nada kansa babban ministan mai, bai kamata ba ya rika zargin wasu da rashin wadata kasar da man fetur.

PDP dai ta ce duk da alkawarin da APC ta yi cewa matsalar karancin man fetur za ta zama tarihi idan ta karbi mulki, halin kuncin da ‘yan Nigeria suka shiga yanzu abu ne da ya nuna an yaudari ‘yan kasar.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com