|| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

[Lyrics] Umar M Shariff Sakatariya

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


172 367

[Lyrics] Umar M Shariff Sakatariya

Shi- Na baki Guri Zauna Acikin Raina Ba Wata Sai Ke

Ita- Na Baka Guri Zauna Acikin Raina Ba Wani Sai Kai

Shi- Na Baki Guri Zauna Acikin Raina Ba Wata Sai Ke

Ita- Ayy Nabaka Guri Zaunaaaaaaa

Shi- haaa Sinadarin Soyayya Ita Zansa Farko Farko
      Sai Hakuri Yabiyo Bayan Haka Sai Ai Karko Karko
      Shayi Wani Keso Wani Ko Yafiso Yaga Koko Koko
      Nike Nai Ra,ayi Acikin Raina Tini Kinka Narke
    Ba sauyin Ra,ayi Nai Alkawari Ba wata Sai Ke

Ita- Ayy Soyayya Innatuna Kaine Nawa Sai Naji Dadi-Dadi
      Bakina Yaki Shuru Wasu Sunce Nacika Kaudi-Kaudi
      Na Dau Maganarsu Zugace Itakesawa Nai Fadi-Fadi
      Nakasa Na Jurewa Wanda Zaya Tabaka Ko Zana Doke
      Nadau Litafinso Kai Dai Nabari Sauran Na Soke

Shi- Ko Raina Ya ‘Baci Naji Muryarki Sai Naji Nayi Laushi
      Komai Kikaban Na Karba Yan Mata Bakya Bani Haushi
      Lamba Daya Gun Tsafta Wacce Kafarta Bata Kaushi-Kaushi
     Masan Ya kusheki Nasan Muryatasa Zata Shaqe
     Tsatsar Kyawunki InKika Biyo Hanya sai Ai Ta Leke

Ita- haa Kamar Kullin Haka Yau Nawayi Gari Da Farin Cikin Masoyi
     Idanu Babu Jiri A Yanayi Jikina Sanyi Sanyi
     Najini Kamar Gimbiya Mai Sarautar Kasaita Da Bayi
     Ammafa Kumin Uziri Acikin Dariyata Inna Sheqe
    Nai Dacen Nagari Ban Barinshi Yakufce Zo Na Chafke

Shi- Na Baki Guri Zauna Acikin Raina Ba Wata Sai Ke
Ita- Na Baka Guri Zauna Acikin Rana Ba Wani Sai Kai

Rubutawa;-

Abubakar Rabiu
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com