Labari da dumi duminsa Sanatoci biyu sun bar jamiyyar APC

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0

Labari da dumi duminsa ya tabbatar da cewa Sanatoci Guda biyu na jamiyyar APC sun bar jamiyyar ya yinda jamiyyar ta rabu gida biyu

Sanatocin sune Shehu Sani da kuma Usman Hunkuyi , inda suka ware bangaren su me suna “AKIDA”

Lokacin da yake jawabi a taron manema labaru a Kaduna, shugaban kungiyar wakilai na jam’iyyar, Tom Maiyashi ya ce shawarwari suna tafiya tare da wasu jam’iyyun siyasar da kuma yanke shawara kan inda za su koma nan da  mako guda ko biyu ”

Maiyashi ya ce, shuwagabannin biyu ba su halarci taron manema labaran ba, saboda matsalolin tsaro “tun lokacin da aka kai su hari a cikin taron manema labaru biyu da suka gabata a cikin Kaduna”.

Ya ce jam’iyyar ba ta da mulkin dimokra] iyya na cikin gida, kuma ya kasa cimma burin da ‘yan Nijeriya ke bukata.

Ku kasance damu Dan Cigaban Labarin
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.