Ko Meyasa Nafisa Abdullahi Ta Caccaki Ali Nuhu Kan Ziyara Bukola Saraki

1

Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Nafisa Abdullahi ta caccaki jarumi Ali Nuhu bisa jagorantar wata tawagar mambobin masana’antar shirya fina-finan Hausa, domin kai wata ziyara ta musamman ga shugaban majalisar dattawan kasar nan, Dr Abubakar Bukola Saraki.

Jarumar ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda jarumin ya kwashi wasu mata wadanda a cewarta bata taba ganinsu ba a rayuwarta, ballantana ma ace ‘yan masana’anatar Kannywood ne, inda ya sanyasu a tawagar da sunan ‘yan fim ne, domin kai waccan ziyara ga Saraki.

Nafisa ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a yammacin jiya Laraba.

Tunda fari dai, fitacciyar jaruma Rahma Sadau ce ta sanya hotunan jarumi Ali Nuhu da sauran matan da suka kai waccan ziyara a shafinta na Twitter tana mai cewar matan tamkar wasu kusoshi ne a masana’antar.

Nan da nan, Nafisa ta mayarwa da Rahmar martani tana mai cewar wadannan mata fa basa cikin masana’antar, tana mai cewar ire-iren wadannan dabi’u na ware cikakkun ‘yan masana’antar daga gudanar da sabgogin da suka shafi Kannywood din shine abinda ke haifar da koma baya ga ci gabanta.

#Saugraph
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

1 Comment
  1. YUSUF ALI says

    This is ur on wahala , why not u will not vist BUHARI Bcs he is good man and he will not give u something. U visit bokola at what rezing bcs he help Kano or he is d one who prove firm village, my advice to you, u can visit people who helped Nigeria, like BUHARI or K IDIRIS or BURTAI or HAMID ALI or this man in E. F. C. C. which i forgot his name, sorry MAGU Bcs this is the good people we now in Nigeria i love them

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.