|| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Jonathan Zai Jagoranci Tawagar Masu Sa Ido A Zaben Liberiya

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0 111

Daga Umar A Hunkuyi

 Tsohon Shugaban Kasar Nageriya, Goodluck Ibele Jonathan, ne zai jagoranci tawagar masu sanya ido a zaben raba-gardaman Kasar Liberiya.

A cikin wata sanarwa da ta fito daga Ofishin hulda da manema labarai ta tsohon Shugaban, ta bayyana cewa, tsohon Shugaban zai jagoranci tawagar masu sa idon da za su taho daga Kasar Amerika, Cibiyar kula da Dimokuradiyya ta kasa, Kungiyar tawagar masu sa ido a kan zabe ta Duniya a zaben raba-gardaman da za a yi a kasar ta Liberiya, ana dai sa ran tawagar masu sa idon za ta isa Monrobiya babban birnin na kasar Laberiya ne a ranar Lahadin nan ta jiya.

A ranar 26 ga watan Disamba 2017, ne dai aka shirya gudanar da zaben.

Bayanin ya nu na cewa za a fafata ne a tsakanin dan takarar Jam’iyyar da ke kan mulki ta kasar, da kuma mataimakin Shugaban kasar mai mulki yanzun, Joseph Nyumah Boakari, da kuma dan Jam’iyyar adawa ta CDC, tsohon shahararren dan kwallon kafar nan ta Duniya, George Weah.

Jawabin wanda mai baiwa tsohon Shugaban na Nijeriya shawara a kan harkokin manema labarai, Mista Ikechukwu Eze, ya sanyawa hannu, ta nu na cewa, tawagar masu sa idon wacce take  kumshe da wakilai 35, tana kumshe ne da ‘yan siyasa, kwararru a kan harkar zabe da kuma wasu kwararrun da za su fito daga kasashen Afrika 18, Turai da kuma Arewacin Amerika, ta hada har da Atifete Jahjaga, tsohon Shugaban kasar Kosobo, Hanna Tetteh, Tsohuwar Minstan harkokin waje na kasar Ghana da kuma Shugaban masu sa idon na wannan shiyyar, Dakta Christoher Fomunyoh.

Bayanin ya nu na Jonathan na cewa, “Ina alfahari da kasancewa jagoran wannan hamshakiyar tawaga, wacce za ta yi tsayin daka wajen tabbatar da an gudanar da zaben a bisa gaskiya da cancanta cikin zaman lafiya da lumana a kasar ta Liberiya, musamman a bisa la’akari da yadda zumunta da kuma kusanci yake a tsakanin kasata Nijeriya da kuma kasar ta Liberiya.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com