Jarumar Nollywood, Omoni Oboli, Ta Sauka A Kano Domin Bincike

0

Jarumar Nollywood, Omoni Oboli, ta sauka a Kano shekaranjiya cikin shigar Hausawa domin gudanar da gwaji (audition) na ‘yan wasan da za ta saka a sabon fim ɗin ta.

A cewar ta, fim ɗin zai ƙunshi ‘yan wasan Arewa da na Kudu, kuma za a riƙa magana da Hausa da Turanci a cikin sa.

An yi wannan gwajin jiya a gidan wasanni da motsa jiki na Ahmed Musa Sport Centre da ke Hotoro, Kano.
Omoni Oboli ita ce marubuciyar littafi mai suna “The Stars are Ageless”.

#Fimmagazine
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.