Jami`an Tsaron Najeriya Sun Binciki Atiku Bayan Dawowarsa Daga Dubai

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

BABBAN LABARI: Jami’an tsaron Najeriya ‘sun binciki Atiku’ bayan dawowarsa daga Dubai.

Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP mai hamayya, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa jami’an tsaron kasar sun bincike shi ranar Lahadi jim kadan da isarsa Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya koma kasar ne daga birnin Dubai inda ya shafe kwana da kwanaki tare da wasu abokan siyasarsa da kuma mukarrabansa.

Bai yi ƙarin bayani kan dalilin da ya sa aka bincike shi ba.

Kawo lokacin wallafa wannan labarin hukumomi ba su ce uffan ba.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Alhaji Atiku Abubakar ya ce jami’an tsaron sun dauki matakin ne da zummar yi masa barazana.

Atiku Abubakar ya wallafa cewa:

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 702

A cewarsa, “Na iso Abuja da safiyar nan inda jami’an tsaro suka bincike ni da zummar yi min da ma’aikatana barazana.”

“Na sha alwashin gina Najeriya yadda babu wani jami’in tsaro da ake biyansa da kudin ‘yan kasar domin ya kare su zai rika yi musu barazana,” in ji Atiku.

Rahotanni sun ce Alhaji Atiku Abubakar ya je Dubai ne domin hutawa da kuma gudanar da taruka na siyasa gabanin soma yakin neman zabe ranar 13 ga watan Nuwamba.

#CnnHausa

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: