JAMB Ta Dakatar Da Ma’aikaciyar Da Ta Ce Maciji Ya Hadiye Miliyan 36

0 351

A ranar Lahadin nan ne, Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasarnan JAMB, ta bayar da sanarwar dakatar da ma’aikaciyar nan na ta mai suna, Philomina Chieshe, wacce ta yi ikirarin cewa wai, wani gardeden maciji ya hadiye tulin takardun kudi na Naira jimillan Naira milyan 36, a Ofishinta da ke Makurdin Jihar Benuwe.

Shugaban sashen sadarwa na hukumar ne, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan ga wakilinmu a ranar Lahadin da ta gabata, ya kuma kara da cewa, baccin dakatarwar akwai wasu matakan ladabtarwa da za a dauka a kanta, sa’ilin kuma da jami’an tsaro ke ci gaba da bincikan lamarin.

Kamar dai yadda ma’aikaciyar, Chieshe, ta zayyana a bayaninta, tana zaune ne kwatsam sai ta ga wani narkeken maciji ya shigo ofishin nata a tashi guda kwalam ya lankwame tulin takardun kudin har Naira milyan 36.

Hukumar ta JAMB, ta bayyana cewa, kudin sun fito ne daga cinikin sayar da katukan duba jarabawa ne na Jihar da kuma wasu hanyoyin tara kudade na hukumar.

Related Posts

Faruwar hakan dai ya tilastawa hukumar ta JAMB, tura jami’anta masu binciken kudi dukkanin rassanta na Jihohin kasarnan, domin su karbo mata duk cinikin da aka yi, da kuma sauran katukan da ba a sayar ba,domin magance wani abu mai kama da hakan.

Da farko dai matar, ta shaidawa masu bincike ne cewa, ba ta san inda kudin hukumar da ta tara milyan 36 a ofishin na ta ta hanyar sayar da katin duba jarabawar a shekarar da ta gabata suka shiga ba.

Amma da ta dan kara jin makaran masu bincike, sai ta yi kokarin canza maganan na ta, inda ta kuma ce wai, yarinyar da ke yi mata hidima a gida ne ta hada kai da wata makwabciyarta mai suna Joan Asen, inda suka sace kudin daga akwatin karfen ajiyar kudin da ke cikin ofishin na ta ta hanyar siddabaru.

Sai dai kuma, a yanzun haka Hukumar EFCC, ta shiga cikin lamarin inda ta fara bincikar inda gaskiyar maganan take, a bisa umurnin da gwamnatin Tarayya ta ba hukumar ta EFCC, a shekarar da ta gabata, na ta binciki ayyukan hukumar shirya jarabawar JAMB.

#hausaleadership
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com