Ikon Kwace kadarori: Dalilin Da Ya Sa Zamu Raba Shugaban Kasa Da ikonsa -Majalisa

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0

Ikon Kwace kadarori: Dalilin da ya sa zamu raba Shugaban kasa da ikonsa – Majalisa

Majalisar wakilai za ta mayar da ikon kwace kadarorin masu laifi daga hannun Shugaban kasa, Muhammad Buhari zuwa ga Alkalan manyan kotunan kasar.

Shugaban majalisar, Yakubu Dogara ya ce sun yanke wannan shawara ne domin hakan zai karfafawa bangarorin gwamnati guiwa ta yadda za su gudanar da ayyukansu kamar yadda tsarin mulki ya tanada tare kuma kara baiwa tsarin dimokradiyya gindin zama.

Sai dai wasu na ganin wannan mataki da majalisar ke shirin dauka bai rasa nasaba da umarnin Shugaba na musamman na kwace kadarorin da aka mallaka da kudaden rashawa wanda Buhari ya rattaba hannu a kai kwanan nan.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.