|| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Hakika Masana’antar Kannwood Daukaka Sanadiyar Wasu Abubuwa

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0 604

Kannywood Hakika masana’antar Kannywood ta samu farin jini da daukaka sanadiyar ire-iren damar da take baiwa masu basirar yin waka ko fitowa a wasan kwaikwayo.

Wannan dandalin ta cigaba da bunkasa martaban arewan ta hanyar wasanni don nishadantarwa da fadakar da jama’a da labarurruka masu kayatarwa.

A cikin shekara ta 2017 Kannywood ta samu canji ko kuma ince ta fara sauya yadda aka saba ganin fina-finan ta sanadiyar kaddamar da tsarin Box office wanda zai taimakawa wajen haska fina-finai a sinimomi da gidajen kallo.

Hakazalika masu ruwa da tsaki na masana’antar sun gyara fuskar yadda suke shirya fina-finai inda a halin yanzu suna takama da kayan aikin fasahar zamani wajen shirya fim.

Jaruman masana’antar Kannywood 6 da suka yi tasiri cikin 2017 

A 2017 kannywood ta samu wasu sabbin jarumai tare da tsoffin jarumai matasa wadanda tauraron su ke haskawa »

Ga wasu cikin su muna iya cewa sun shigo masana’antar da kafar dama yayin da sauran ke jajircewa wajen bayyana basirar su bainar jama’a.

Ga jerin jarumai wanda muke ganin cikin 2018 gwanintar su da kuma nuna fasahar su zai janyo haske ga tauraron su a masana’antar.
Munyi masu lakabi da “Manyan Gobe”;

1. Maryam Yahaya
Bana wannan jaruma tana sahun gaba cikin jarumai da tauraron su ya haska.
Bayan fitowar ta shirin “Mansoor” » ta cigaba da nuna mana irin basirar dake tattare da ita wanda suma masu shiryawa fina-finai suka shaida hakan har ma suke ta haska ta a fina-finai daban daban.

2. Rashida Lobbo
Bana dai wannan jarumar ta samu kyautar city people awards » a jihar legas bisa ga rawan da ta taka a masana’antar Kannywood.

3. Amal Umar
Amal tana cikin yan wasa da suka yi fice acikin shirin MTV “shuga” wanda ake yi cikin harsheb turanci. Banda haka jarumar ta fito a fina-finai da dama na masana’antar kannywood.

4. Umar M.Sheriff
Fitaccen mawaki Umar M.Sheriff ya gwada iyawan shi fitowaer shi a cikin “mansoor” a matsayin jarumi kuma da alama ya ji dadin hakan kuma zai cigaba da damawa a cikin harkar.

5. Halima Ibrahim
Jarumar ta fito a cikin shirin “Rabu da Maza” tare da fitaccen jarumi Sadiq Sani Sadiq da kuma jaruma Amal Umar

6. Garzali Miko
Shima dai wannan mawaki yana tafarkin sauya sheka zuwa fannin fim.

7. Ahmad Illiyas Tantiri
Ahmad daya daga cikin yaran babban direkta kuma mai shirya fim ne watau Abdulmumin Illiyas Tantiri.

Yana daya daga cikin yara dake kokartawa a farfajiyar fim.

Abubuwa 5 da ya faru a masana’antar kannywood cikin 2017 

Ga jaruman bana shekara ce na shirya damawa da sauran fitattun jarumai.
Yayin da muke shirin shiga wata sabuwar shekara na 2018, da fatan dai zasu kokarta a cikin ta.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com