Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Daukar ‘Yan Sanda Dubu 10 Kowacce Shekara

12 30
A yunkurin ta na kawo karshen karancin jami’an tsaro da ake fuskanta a kasar, gwamnatin tarayya ta baiwa rundunar ‘yansanda damar daukar sabbin jami’ai har guda 10,000 a duk shekara.
Babban Sifeton ‘yan sanda, Ibrahim Idris shi ya tabbatar da haka yayin da ya ke jagorantar wani taro na manyan jami’an ‘yan sanda a birnin tarayya Abuja.
Idris ya ce wannan mataki ya zama wajibi idan har za a kawo karshen aikata miyagun laifuka a Nijeriya.
Ya ce a yanzu haka akwai dan sanda daya ga kowanne mutum 400 a Nijeriya, kuma wannan mataki zai taimaka wajen rage wannan alkaluma.
Babban sifeton ‘yan sandan ya kuma yi kira ga majalisa da ta gaggauta sanya hannu a kan kudirin da aka gabatar mata na kara adadin kudaden da ake warewa hukumar ‘yan sandan kasar.Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com