Gwamnatin APC: Abar Yabo Ko Abar Fallasa?

0 119

A fili ta ke cewa, lokacin da mulkin jam’iyyar PDP ya zo karshe a Nijeriya cikin shekara ta 2015, kusan kowa tir da Allah wadai ya ke yi tare da Allah raka taki gona! Bugu da kari, mafi yawa na da kwakkwarar kwarin gwiwar ganin cewa, canji ya samu a kasar, sannan kuma duk datti da su ke zargin PDP ta kawo, sabuwar jam’iyya mai mulki, APC, za ta tsaftace shi.

Idan ka jingine laifuka da dama da talakan Nijeriya ke tuhumar gwamnatin PDP da su a gefe, babban laifin da talakan ke ganin gazawar PDP a lokacin shi ne, matsalar tsaro, saboda ganin yadda kungiyar Boko Haram ta mamaye wasu kananan hukumomi, sannan kuma ta ke kai hare-hare duk inda ta ga dama a fadin kasar, musamman yankin arewacin kasar.

Don haka a ka zabi APC a mataki na tarayya da ma yawancin sauran matakan gwamnati, saboda fata da burin kawo karshen matsalar tsaro a kasar da kuma sauran wahalhalun rayuwa da ta’annati da dukiyar gwamnati. Yanzu an shafe fiye da rabin tafiya an ma fara gangarawa a zangon mulkin APC na shekara shekara hudu, kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya ya wassafa.

Za a iya cewa, kawo yanzu APC ta maganta matsalar tsananin tsaron can da a ke fama da ita. To, amma kada a manta da cewa, a na kafa gwamnati ne saboda dalilai biyu; wato tsaro da walwalar jama’a. Kafin zuwan APC lamarin tsaro ya shiga halin ha’ulahi, amma bayan zuwanta kuma an shiga matsalar walwala ta tsadar rayuwa, wanda wannan shi ne daya ginshikin kafuwa da samar da gwamnati a cikin al’umma.

Abin nufi a nan shi ne, a yayin da PDP ta fadi a bangare guda na rabin dalilin samar da gwamnati ga al’umma, wato ta fannin tsaro, ita ma APC ta gaza ta fuskar samar da walwala da jin dadin rayuwa.

To, amma kasancewar APC ba ta shafe shekarun da PDP ta kwashe ta na tafiyar da mulki ba, ba za a iya yi mu su hukunci iri daya ba.

PDP shekararta 16 ta na rike da akala da madafun ikon kasar, ita kuwa APC a cikin shekara ta uku kacal ta ke. Don haka ko da ba a yaba ba, to za a iya cewa babu yabo babu fallasa, domin akalla ta samar da rabin abinda a ke nema; shi ne tsaro, sauran walwala da jin dadin jama’a.

Bugu da kari, a lokacin baya, kafin zuwan APC, ’yan kasar ba su da kwarin gwiwa a kan gwamnatin tarayya kan satar kudin al’umma daga lalitar gwamnati da kuma cin hanci da rashawa, amma a yanzu za a iya cewa, akalla za a iya cewa, ko babu komai talakan kasar ya yarda da shugaban gwamnatin. Sai dai kuma babban abin takaici shi ne, a sauran matakan gwamnati, kamar jihohi da kananan hukumomi, har yanzu ba ta canja zani ba.

Yadda a baya a ke kallon yawancinsu a matsayin barayin gwamnati kuma masu tafka cin hanci da rashawa, haka nan har yanzu irin kallon da a ke yiwa yawancin nasu kenan, idan ka zare kalilan daga cikinsu.

Har yanzu gwamnoni ba sun daina sarrafa kudaden kananan hukumomi ba bisa ka’ida ba, ita kuma gwamnatin tarayya ta kasa yin komai kan hakan.

Don haka komai ya cigaba da tafiya kare-zube tun lokacin zamanin PDP har kawo yanzu, wanda hakan ya saba da irin alkarin da APC ta yiwa ’yan kasar a lokacin yakin neman zabe. Wannan ba karamin koma-baya ba ne, kuma lallai ya kamata APC ta sani cewa, lokaci ya fara kure ma ta, domin an riga an shiga shekarar jajiberen zabe.

Idan ba ta yi gaggawar yin wani abu kan halin da talaka ke ciki ba, to komai na iya faruwa. Zai iya yiwuwa ta fadi a zaben 2019 ko kuma ta rasa kujeru masu yawa a mukamai daban-daban.

Tun da sanyin safiya dai a ke kama fara, domin tuni an shiga jajiberen shekarar zabe!

#Hausaleadership
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com