EFCC Ta Kama Makudan Kudade Kusan Naira Miliyan 49 A Tashar Jirgin Saman Kaduna

0 55
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar EFCC ta samu wasu makudan kudade da yawansu ya kai Naira miliyan 49 a filin tashan jirgin saman Kaduna,  hukumar ta ce hakan na nuna irin nasarar da ake samu a yaki da cin hanci a Najeriya.
Jami’in hukumar ya ce bayanai ne da suka samu na tsegumi suka nuna akwai kudi da aka boye a buhuna, dalili da ya sa suka garzaya inda suka samu kudin.
Wison Uwujeren, Jami’in labarun hukumar EFCC ya yi wa manema labarai karin haske akan lamarin karbe kudin da ake ganin na haramun ne.
Ya ce ana ci gaba da samun nasara akan yadda mutane ke tseguntawa hukumar inda aka boye kudin da aka tara ta hanyar ba ta dace ba, a yayin da a yanzu haka babu wanda ya fito fili ya ce kudadensa ne.Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com