Dalilin Da Ya Sa Shekau Ya Kashe Kakakin Sa

2 12
A wani faifan Bidiyo na tsahon mintina 50 da kamfanin dillancin labaran AFP ya ce ya na yawo a tsakanin mayakan Boko Haram, Shekau ya bayyana cewa ya kashe kakakin sa da aka fi sani da Abu Zinnira.
Abu Zinniri dai ya sha fitowa a fai-fan bidiyon mayakan sanye da kaki da rawani, ciki har da na garkuwa da ‘yan matan Chibok.
A faifan, shekau ya bayyana cewa ya kashe Zinnira ne a sakamakon shirya masa makarkashiyar kifar da shi daga mukamin shugabancin kungiyar da ya yi.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya dai na ci gaba da yakar mayakan na Boko Haram wadanda suka watsu a gari bayan sun tarwatsa maboyarsu da ke dajin Sambisa. Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com