Badakalar Naira Miliyan 124: EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Ma’aikacin Banki

0 128

A ranar Litinin data wuce ne, Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) dake shiyyar Ibadan ta gurfanar da wani tsohon ma’aikacin Banki Adejare Sonde a gaban Babbar Koto dake garin Abeokuta a cikin ta jihar Ogun   a bisa tuhuma guda sha biyu akan zargin satar kimanin naira miliyan 124 da yin bugi da kuma canza alkalumman wni kundaye.

Wanda ake tuhumar, ya gurfana ne a gaban Alkali mai shari’a A.A Akinyemi,inda wanda ake tuhumar, ya amsa laifinsa akan zargin da ake yi masa. Lauyan na EFCC Cosmos Ugwu ya roki kotun data sanya ranar da za a ci gaba da shari’ar ya kuma roki Kotun data sa ajiye wanda ake zargin a gidan Yari.

Sai dai, shi kuwa lauya mai kare wanda ake tuhumar, E. E. Jacob ya sanar da Kotun cewar, tuni an gabatarwa da Kotun takardar bayar da belin wanda ake tuhuma.

Related Posts

Majalisa Ta Yi Allah Wadai Da El Rufa’i Kan Rusa Ofishin…

Jacob ya kuma roki Kotun data bari wanda ake tuhumar yaci gabada zama a ma’ajiyar hukumar ta EFCC, har zuwa lokacin da za a saurari takardar ta bayar da belin wanda ake tuhumar.

Alkalin Kotun Mista  Akinyemi ya amince da rokon lauyan da yake kare wanda ake tuhuma, na cewar a ajiye shi a ma’ajiyar ta EFCC, har sai an saurari takardar bayar da belin.

An kuma daga sauraron karar zuwa ranar Juma’a 16 ga watan Fabarairun shekarar 2018 don ci gaba da sauraron karar da kuma sauraron takardar ta bayar da belin wanda ake tuhuma.

#Hausaleadership
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com