An Kashe Miliyan 28 A ‘Juyin Sarauta’ Amma Ganduje Bai Taimake Mu Ba –Ramat

0

LABARAIWASANNIRAHOTANNISIYASAKASUWANCIADABIRA’AYINMUTATTAUNAWABIDIYOMAKALAR YAU CONNECT WITH US Leadership Hausa Newspapers BIDIYOAn Kashe Miliyan 28 A ‘Juyin Sarauta’ Amma Ganduje Bai Taimake Mu Ba –RamatPublished 3 days ago on June 10, 2018 By Nasir S Gwangwazo Fim din Juyin Sarauta, wanda fitacciyar marubuciya kuma furodusa, BALARABA RAMAT YAKUB, ta dauki nauyi ya zama zakaran gwaji tun gabanin fitowarsa a kasuwa, inda ya ke ta lashe kambu a duk gasar da a ka shiga da shi. Ya zama gwarzon fim na yarukan cikin gida a Najeriya a gasar Zuma Film Festibal Awards da a ka gudanar watannin baya, wato Best Indigenous Language Film’, inda ya bai wa finafinan Yarabanci da na Ibo kashi a gasar. Bugu da kari, ya samu fitowa a manyan rukunan gasa guda 14 na AMMA Awards Season 5 da a ka gudanar kwanakin baya, inda ya lashe guda shida daga ciki, wadanda su ka hada da Gwarzon Jarumi wanda Ado Ahmad Gidan Dabino ya lashe, Gwarzon Kirkirarren Labari wanda Balaraba Ramat Yakub ta lashe, Gwarzon Mai Daukar Hoto wanda Nasiru Dorayi ya lashe, Gwarzon Tsara Dandali wanda Aliyu Shehu Yakasai da Abubakar S. Reshe su ka lashe.

Gwarzon Tsara Dandali wanda Aliyu Shehu Yakasai da Abubakar S. Reshe su ka lashe. Sai kuma Gwarzon Kidan Taushi wanda Habibu Lafazi da Ibrahim Danko su ka lashe, sannan Gwarzon Siddabaru wanda Ali Musa Danjalo da Faruk Sayyadi su ka lashe. Haka nan sauran guraben da ya samu fitowa (nominations) sun hada da Gwarazan Kwalliya, Sauti, Sutura, Hada Hoto, Mataimakin Jarumi, Mataimakiyar Jaruma, sai kuma Gwarzon Fim da Gwarzon Darakta. Ganin irin wannan gagarumar nasara da Juyin Saraura ke samu, Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya tuntubi Hajiya Balaraba Ramat, don jin sirrin boyen. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ko za ki iya gaya wa masu karatu abinda labarin Juyin Sarauta ya kunsa a takaice?

Labarin fim din an gina shi ne kan Sarauta da yadda matan sarakai da kwarakwaransu su ke juya akalar kowane irin abu a farfajiyar gidan sarakai. Sau tari za ka ka ga har warware abin da a ka zartar a fada su ke yi kuma su aiwatar da nasu, kuma dole a tafi a haka ko da sanin sarakunan ko kuma babu saninsu.

Me ya dauki hankalinki ki ka zabi labarin Juyin Sarauta a matsayin wanda za ki shirya?

Labari ne na mulki irin na mata, inda kowacce ta gwada isarta da iya mulkinta tare da iya shiga da fita a gurin bokaye da malamai da kuma ‘yan tsubbu.

Wannan ne ya ja hankalina, domin saurata ta mai rabo ce kuma ba a sarki biyu a gari daya. Ko masu nema sun kai dari, to dai daya ne zai hau.   Da alama an kashe makudan kudi wajen shirya shi.

Shin ina ki ka samo irin wannan kudi haka a lokacin da a ke tsoron kashe wa finafinai kudi, saboda faduwar kasuwa?

Gaskiya shirin ya lashe kudi masu yawan gaske. Ma’aikatar kudi ta tarayya ta ba mu tallafin Naira miliyan bakwai. Mun ranto miliyan takwas da dubu dari biyar a gurin banki kasuwanci, sannan kamfanin Ramat Production Limited da Dogarai Kuarters Women su ma sun zuba kudade da yawa a ciki.

Nawa a ka kashe zuwa yanzu?

Mu na hasahen wajen miliyan ashirin da takwas ta dulmiya.

#Hausaleadership
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.