| Gidan Wakokin Hausa A Duniya

Akwai Yiwuwar Messi Ya Fi Ronaldo Kokari A Wannan Kakar

Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo


0 207

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Argentina da Barcelona, Lionel Messi ya ci kwallo 22 a kakar bana ta kakar wasa ta 2017 zuwa 2018.

Messi mai shekara 31 ya fara zura kwallo ne a bana a karawar da Real Madrid ta doke Barcelona 3-1 a gasar Spanish Super Cup da suka kara a Nou Camp a ranar 13 ga watan Agustan  wannan shekarar 2017.

sannan  dan wasan na Argentina ya ci kwallaye biyu a fafatawar da Barcelona ta ci Alabes a ranar 26 ga watan Agustaa gasar La Liga a wasan farko na gasar ta bana.

Jumullar kwallo 22 Messi ya ci a kakar bana, 15 a gasar La Liga ya ci wa Barceloa, da hudu da ya zura a raga a gasar cin kofin Zakarun Turai da ukun da ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Argentina a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da za’ayi a kasar Rasha.

Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga, za kuma ta buga wasan zagaye na biyu a gasar cin Kofin Zakarun Turai bayan da aka hadata da kungiyar chelsea sannan Argentina za ta je gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 inda ta fito a rukunin daya hada da kasar Najeriya da Crotia da kuma Iceland.

Dan wasan ya lashe kyaututtuka da dama a kungiyarsa ta Barcelona sannan ya lashe kyautar dan kwallon duniya sau biyar a tarihi.

Har ila yau dan wasan yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a tarihin kungiyar ta Barcelona sannan kuma ya zura kwallo a ranar Lahadi a wasan da suka doke Real Madrid daci 3-0 a gasar laliga.
Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com