Aguero ya ci Liverpool karo na 5 a jere a Premier a Ettihad

0 23
 
Manchester City da Liverpool sun raba maki dai-daya a tsakaninsu, bayan da suka tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar Premier mako na 29 da suka yi a ranar Lahadi.
Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun James Miller a bugun fenareti kuma kwallo na bakwai kenan da ya ci a bugun daga kai sai mai tsaron raga a kakar Premier nan.
Manchester City mai masaukin baki ta farke ta hannun Sergio Aguero, wanda karo na biyar kenan yana cin Liverpool a filin Ettihad. 
Da wannan sakamakon Manchester City tana mataki na uku a kan teburin Premier da maki 57, yayin da Liverpool ke matsayi na hudu da maki 56. Kuna Iya Bibiyarmu Ta Shafukan Sada Zumunta
Shafin Sada Zumunta Na Facebook Page
Shafin Sada Zumunta Na Twitter

Leave A Reply

Your email address will not be published.

WordPress spam blocked by CleanTalk.
Social Media Auto Publish Powered By : XYZScripts.com